Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ya bayyana cewa an lalata aƙalla manyan turakun wutar lantarki guda 10 cikin watanni biyar a Jihar Kano, lamarin da ke barazana ga samar da ingantacciyar wutar lantarki a jihar da kewaye .
Manajan TCN mai kula da Kano, Injiniya M.K. Bello, ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin wayar da kan jama’a kan illolin lalata kayayyakin wutar lantarki, wanda aka gudanar a garin Paki da ke Ƙaramar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna.
A cewarsa, turakun da aka lalata suna kan manyan hanyoyin wutar lantarki da suka haɗa Kano da Zariya, Kano da Katsina, da kuma Kano da Hadejia.
Injiniya Bello ya ce, da taimakon al’umma, an kama mutane sama da 33 da ake zargi da hannu wajen lalata kayayyakin wutar lantarki.
A nasa jawabin, Mataimakin Babban Manajan TCN, Injiniya Ibrahim Aliyu, ya bayyana cewa satar kayayyakin ƙarafa da lalata turakun lantarki na ƙara zama babbar barazana ga kayayyakin kamfanin da kuma samar da wutar lantarki.
Ya buƙaci jami’an tsaro da su tabbatar da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu, domin hukunta duk wanda aka samu da laifi tare da hana wasu aikata irin wannan ta’asa.
A nasa ɓangaren, Kauran Zazzau kuma Hakimin Paki, Alhaji Ja’afaru Aliyu Paki, ya yaba wa kamfanin TCN bisa shirya gangamin wayar da kan jama’a a yankin.
Hakimin ya tabbatar da cewa al’ummarsa za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro wajen kare kayayyakin gwamnati, musamman na wutar lantarki da layin dogo, daga masu lalata su.
