Babbar Kotun Jihar Adamawa da ke zamanta a Yola ta soke tarukan gangamin Jam’iyyar ADC da aka gudanar a jihar ranar Litinin.
A hukuncin da Mai Shari’a Isah Ahmed ya yanke, ya bayyana cewa taron bai inganta ba saboda karya ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
Kotun ta ce taron ya saɓa wa Sashe na 84(4) na Dokar Zaɓe da kuma Sashe na 18 na kundin tsarin mulkin ADC, don haka ya zama haramtacce.
Alƙalin ya ƙara da cewa waɗanda ake tuhuma sun yi watsi da ƙa’idojin da aka tanada, suka rungumi abin da ya kira “ƙa’idojin da suka ƙirƙira da kansu.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Shugaban ADC na Jihar Adamawa, Kwamred Shehu Yohanna ya shigar, inda ya ƙalubalanci taron bisa rashin bin doka da tsarin jam’iyya.
Da yake mayar da martani, tsohon sakataren yaɗa labarai na ADC, Martins Dickson, ya ce jam’iyyar ta karɓi hukuncin kotu da hannu biyu, tana kuma jiran umarnin shugabancin jam’iyyar na ƙasa a Abuja kan matakin da za a ɗauka.
