Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ba da umarnin kama wani ɗan kasuwa da ake zargi da sayar da abincin yara masu fama da matsanancin ƙarancin abinci (RUTF), wanda gwamnati ke rabawa kyauta.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayar da umarnin a ranar Lahadi bayan gano kayayyakin a hannun mutumin yayin wata ziyarar duba yadda ake rarraba kayan lafiya a cikin birnin Kano.
A yayin ziyarar, jami’an gwamnati sun kama mutumin da aka bayyana sunansa da Surajo Ibrahim, wanda ke sayar da busassun kayan abinci a yankin Kofar Dawanau da ke kan titin jami’ar Northwest
Jami’an tsaro da na lafiya sun fara bincike domin gano yadda aka karkatar da kayan daga ma’ajiyar gwamnati zuwa hannun ɗan kasuwa.
Ana kuma ƙoƙarin gano ko akwai wasu mutane da ke da hannu a cikin badakalar
Hukumar lafiya ta jihar ta ce za ta ƙara tsaurara sa ido a wuraren rarraba kayan, tare da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi, domin tabbatar da cewa kayan sun isa ga waɗanda aka tanada wa.
