Hukumar kula da harkokin magunguna ta ƙasa, Pharmacy Council of Nigeria (PCN), ta rufe shagunan sayar da magungunan Chemist da ke Kasuwar Kurmi a wani mataki na bazata.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya shafi kafatanin shagunan sayar da magungunan da ke kasuwar.
Kan wannan batu, Premier Radio ta tuntubi shugaban kungiyar ’yan magungunan domin jin ta bakinsa, sai dai ya ƙi cewa komai dangane da lamarin.
Wani shaidar gani da ido wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa tuni aka fara ganin hukumar na sake buɗe wasu daga cikin shagunan da aka rufe.
Sai dai ya yi zargin cewa ana zargin wasu daga cikin masu shagunan sun biya kuɗi domin a buɗe musu, duk da cewa babu wata hujja a hukumance da ta tabbatar da wannan zargin.
