Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar a matsayin karamin abu da ba zai yi wani asiri ba.
Kakakin na ADC ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise ranar Litinin.
Bolaji Abdullahi ya amince cewa a kashin kansa bai ji daɗin tafiyarsu ba, sai dai ya lura cewa hakan ya zo da wani mataki na sauƙi.
Ya ce “Yanzu za mu iya mayar da hankali kan yin abubuwan da ya kamata mu yi ba tare da fuskantar matsin lambar da suke ƙoƙarin sanya mu a ciki ba”.
