‘Yan bindiga sun kashe limamin wani ƙauye da wasu mutum uku tare da yin garkuwa da mazauna garuruwa 12 a wani sabon hari da suka kai a ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai ne da tsakar dare, inda suka fara kai farmaki gidan limamin ƙauyen kafin su kashe shi.
Daga nan suka da harbe wasu matasa uku da suka ƙi bin su bayan sun umarce su da su raka su.
Bayan kashe mutanen, maharan sun yi garkuwa da mutane 12, ciki har da mata da sauran mazauna yankin, sannan suka tsere da su zuwa inda ba a sani ba.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin waɗanda aka harba sun samu munanan raunuka, kafin daga bisani a garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
