Jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Gombe bayan ta lashe dukkan kujeru 24 na shugabannin ƙananan hukumomi da kuma kujeru 240 na kansiloli a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe Abdullahi Garba, ne ya sanar da sakamakon zaɓen, inda ya ce APC ce ta yi nasara a dukkan ƙananan hukumomin da aka gudanar da zaɓen.
Garba ya ce jam’iyyu da dama sun shiga zaɓen, amma APC ce kaɗai ta tsayar da ‘yan takara a dukkan ƙananan hukumomi 24, yayin da wasu jam’iyyu suka fafata ne a kaɗan daga cikin ƙananan hukumomi da gundumomi.
