Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu kan yunƙurin amfani da kotu wajen soke rajistar jam’iyyar NDC, yana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata da mai magana da yawun Atiku Paul Ibe ya fitar.
Sanarwar ta ce Atiku ya bayyana cewa bayan komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya, ba mu taɓa ganin shugaban ƙasa da ya zama maƙiyin dimokuraɗiyya kamar Bola Tinubu ba.
Ha kuma Atiku zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa domin kafa mulkin jam’iyya ɗaya gabanin zaɓen 2027.
