Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da sahihancin shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, tare da yin watsi da ƙarar da ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya shigar.
Mai shari’a Musa Liman ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, inda ya ce ƙarar ba ta da tushe a shari’a, saboda kotu ba ta da hurumin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyya.
Kotun ta kuma amince da ƙorafe-ƙorafen farko da jam’iyyar ADC, tsohon shugaban jam’iyyar Ralph Nwosu, David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola suka gabatar, tana mai cewa Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba.
Haka kuma, kotun ta ce Abejide bai fara amfani da hanyoyin sasanci na cikin gida da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada kafin ya garzaya kotu ba.
Mai shari’ar ya yanke hukunci cewa miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa taron masu ruwa da tsaki na ranar 2 ga Yulin 2025 ya share fagen taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ranar 29 ga Yulin 2025, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanya ido a kansa, kuma a cikinsa aka zaɓi David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare na ƙasa.
Saboda haka, kotun ta ayyana cewa zaɓen David Mark da Aregbesola ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Dokar Zaɓe ta 2026 da sauran dokokin da suka dace.
Kotun ta kuma umarci Leke Abejide ya biya naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara, sannan ta ci tarar lauyansa naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.
Abejide ya shigar da ƙarar ne yana neman kotu ta soke miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark da Rauf Aregbesola, tare da hana INEC amincewa da su a matsayin shugabannin jam’iyyar ADC.
