Kwamandan bataliya ta 242, Monguno, Col. I.A. Mohammed da sojoji akalla 10 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wasu bama-bamai da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka binne a karamar hukumar Monguno ta jihar Borno.
Jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta arewa maso gabas, Sani Uba, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin.
Ya ce maharan sun kaddamar da harin ne a daren Lahadin da ta gabata kan sojoji a cibiyar Charlie 13.
Ya kara da cewa sojojin sun dakile harin ne bayan wani kazamin artabu da suka yi da su, lamarin da ya tilasta wa maharan yin nasaran ja da baya.
Uba ya ce, kwamandan rundunar, a yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa inda dakarun suke domin tantance halin da ake ciki, ya ci karo da bama-bamai da suka tarwatsa motarsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa tare da sojoji shida.
