Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta jinjinawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen rage ƙarancin ma’aikatan lafiya da inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Wakilin WHO a Kano, Dr Sunusi Abubakar Mayana, da wakilin UNICEF, Dr Muhammadu Damish, ne suka bayyana hakan yayin bikin ƙaddamar da rabon takardun aiki ga sabbin ma’aikatan lafiya 2,037 da gwamnatin jihar ta ɗauka.
Dr Mayana ya ce ɗaukar ma’aikatan na nuna aniyar gwamnatin Gwamna Abba na cike gibin da ake da shi a ɓangaren lafiya, yana mai cewa tasirin matakin da gwaman ya ɗauka zai shafi iyalai da dama a faɗin jihar.
Shi ma wakilin UNICEF ya yabawa gwamnatin jihar kan yunƙurin ta na bunƙasa ma’aikatan lafiya da ƙarfafa tsarin, yayin da ƙungiyar likitoci NMA ta jinjinawa Gwamna Yusuf kan sauye-sauyen da ake samu a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kuma manyan asibitoci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, Ƙungiyoyin ma’aikatan jinya da ungozoma, ma’aikatan lafiya da kuma masu hada magunguna sun ce matakan za su taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a Kano, tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi a fannin na lafiya.
