Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoWanene marigayi MK Ahmad?

Wanene marigayi MK Ahmad?

Date:

Da safiyar Asabar din da ta gabata ce, aka wayi gari da labarin rasuwar Alhaji MK Ahmad, wanda ya cika a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya.

 

Marigayin, wanda shine tsohon sakataren jam’iyyar NEPU, ya rasu yana da shekaru 96 a duniya.

 

Ya bar mace daya, da yaya 30 da kuma jikoki.

 

Wanene marigayi MK Ahmad?

 

An haifi Alhaji M.K Ahmad a shekarar 1933, a garin Lokoja dake Kabba, wato jihar Kogi a yanzu.

 

Mahaifiyarsa, Malama Hassana, ‘ya ce ga babban limamin Lokoja Mallam Ibrahim Manko.

 

Ya fara karatun addini a hannun Marigayi Mallam Sule, wanda ‘da ne ga Mallam Yero dake Unguwar Hamza.

 

Daga nan, MK ya fara karatun boko a Church Missionary Society, wadda a yanzu ake kira da Kwalejin Ajayi.

 

Cigaba da karatun sakandire, shine makasudin zuwan sa jihar Kano, inda ya shiga makarantar sakandire ta ‘Danwailare, wato Kano Holy Trinity a wancan lokacin. Bayan ya kammala ne kuma, ya nemi gurbin karatu a London, inda ya sami takardar Diploma a 1964.

 

A shekarar 1980, MK ya sake tsallakawa kasar Amurka, inda ya sami gurbin karatu a jami’ar Century dake Los Angeles, inda ya nazarci harkokin kasuwanci, kuma ya kammala a 1986.

 

Kafin nada shi a matsayin sakataren NEPU  a shekarar 1961, MK Ahmad ya kasance a mukamin sakataren yada labaran jam’iyyar, wanda kuma shima, ya biy bayan kusancin da ya samu da marigayi Mallam Aminu Kano, inda ya taba zama sakataren sa.

 

A tsawon shekaru 96 da ya kwashe a duniya, MK  yayi aiki a ma’aikatu daban daban, na gwamnati da masu zaman kansu.

 

Shine wanda ya kirkiro hukumar jin dadin alhazai ta kasa a wancan lokacin, wato 1961, ‘Nigerian Pilgrims Welfare Association’, kuma ya zama sakataren ta.

 

Marigayin yayi aiki da rusasshiyar hukumar nan ta samar da wutar lantarki, ECN da NEPA, sai Arab Brothers, da dai sauransu.

 

Har ila yau, shine marubucin littafin ‘Chronicle of NEPU/PRP’, inda yayi bayani game da gundarin manufofin tafiyar jam’iyyun.

 

Ya taba samun lambar yabo ta kasa, mai taken MFR a shekarar 2003.

 

Rasuwar MK Ahmad, wani babban rashi ne ga al’ummar jihar Kano, wadanda ke kallon dattijon a matsayin uba, kuma masanin ta kamata wanda kan bayar da shawarwari game da duk wani al’amari da ya shafi cigaban jama’a, musamman a sha’anin siyasa.

Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada, inda sarakunan Kano da Bich suka jagoranci yi masa sallah.

Da fatan Allah ya yi masa rahama Ameen.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories