Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki ta tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta sanar da hakan bayan ta wallafa takardar shaidar tsayawa takarar Goodluck Jonathan a babban zaɓen ƙasar nan na shekarar 2027.
Farida Umar, Mataimakiyar sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Turaki ta shedawa manema labarai cewa jami’iyyar ta amunce da Goodluck Jonathan a matsayin wanda zai kara da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a zaɓen 2027.
Lamarin ya biyo bayan canjin wurin gudanar da taronta na ƙasa da jam’iyyar ta shirya a Abuja a yau Asabar, 30 ga watan Mayu, bayan da ‘yan sanda suka hana mambobinta shiga A Class Hotel, wurin da aka fara tanada domin gudanar da taron.
Daga bisani jam’iyyar ta sauya wurin taron cikin gaggawa, inda aka kammala shi cikin ƙanƙanin lokaci.
A wajen taron, an gabatar da matakin tsayar da Goodluck Jonathan, wanda aka ce ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan jami’iyyar ta PDP tsagin Kabiru Turaki.
