Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Lawan Najume ya ce Karamar Hukumar sa ce ke kan gaba a Kano wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya da da nagartaccen tsarin sufurin kai daliban yankin makarantu akan lokaci kyauta.
Najume ya bayyana hakan ne lokac in da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce tun bayan hawansa mulki gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai kan bangaren lafiya da ilimi musamman kula da mata masu juna biyu da kananan yara.
Shugaban ya ce a halin yanzu ana gudanar da gwaje-gwajen lafiya kyauta tare da samar da ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu a cibiyoyin lafiya daban-daban da ke fadin karamar hukumar, domin rage mace-macen mata masu haihuwa da jarirai.
Shugaban karamar hukumar ya ce a bangaren ilimi kuwa gwamnatin sa ta samar da mota kirar Safa wadda take daukar daliban makarantun Firamare da sakandiren yankin ya zuwa makarantu tare da dawo da su gida domin ragewa iyaye nauyi da karfafawa yara karfin gwiwar zuwa makaranta.
Lawan Najume ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake baiwa kananan hukumomi, ta hanyar tabbatar da ganin suna samun hakkokinsu da isassun kudaden gudanar da ayyukan ci gaba.
