Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce gwamnonin Jihohi na duba yiwuwar biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 100,000 domin rage radadin halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabardin data gabata, inda ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa, da kuma karancin kudi ga ma’aikatan kasar nan ya sanya su ka duba yuwuwar karin albashin.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi suna tattaunawa da Gwamnatocin Tarayya da kuma kungiyoyin kwadago domin cimma matsaya kan tsarin albashin da zai inganta jindadin ma’aikata.
Shugaban kungiyar ya ce manufar ita ce inganta rayuwar ma’aikata, ba tare da an durkusar da asusun jihohi ba, ta yadda jihohi za su iya ci gaba da gina ayyukan more rayuwa da gudanar da ayyukan gwamnati.
A halin yanzu dai mafi karancin albashi a kasar nan naira 70,000 ne a kowane wata.
Sai dai wasu rahotanni sun ce jihohi da dama da su ka hada da Legas da Ribas da kuma Imo suna biyan albashin fiye da haka a wani mataki na tallafawa ma’aikatan.
A gefe guda kuma Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC na ci gaba da matsa lamba domin sake duba albashin ma’aikatan, inda su ka jaddada cewa ma’aikata sun cancanci albashin da zai iya daukar nauyin rayuwarsu ta yau da kullum.
