Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya ce shi ne ya haƙura da kujerarsa aka bai wa Nasiru Yusuf Gawuna, domin samun masalaha a tafiyar Kwankwasiyya da kuma jami’iyyar NDC.
Sanata Hanga, ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da manema labarai, kan makomar siyasarsa bayan rasa tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Sanatan ya bayyana cewar dama tun farko addu’a suke yi domin samun zaɓin da zai kai su ga nasara.
Rufa’I Hanga, ya ce fatansu shi ne jagoransu Sanata Rabi’u Kwankwaso ya samu nasarar lashe zaban Kano, sannan a sama ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, har zuwa matakin da zai zama shugaban ƙasar nan.
Ya ƙara da cewar duk wanda yake cikin tsarin ya san cewar an yi wa kowane ɗan takara adalci.
Sanata Hanga ya jadadda mubaya’arsa ga Kwankwaso, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa da shi a kowane lokaci.
Sanatan ya ce da su aka yi shawara kan takarar da aka bai wa mutane, kuma da saninsa aka ba wa Nasiru Gawuna takarar kujerarsa.
