Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani kwamitin mutum 11 domin gano gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba tare da duba sahihancin amincewar gine-gine a cikin birnin Kano.
Sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim, ya ce aikin kwamitin na da muhimmanci wajen bunƙasa ci gaban muhalli, tattalin arziki da tsara birane yadda ya kamata a jihar.
Ya bayyana damuwar gwamnati kan yadda ake ci gaba da gina-ginen ba tare da samun izini ba, yana mai cewa hakan na kawo barazana ga ci gaban birane da lafiyar al’umma.
Kwamitin wanda Darakta Janar na KANGIS, Dakta Dalhatu Aliyu-Sani zai jagoranta, an ɗora masa alhakin gano gine-ginen da ba bisa ƙa’ida ba a ƙananan hukumomin Nasarawa, Tarauni, Kumbotso da Fagge, tare da nazarin duk wasu takardun izinin gini da aka bayar cikin shekara guda da ta gabata.
An kuma umurci kwamitin da ya bayar da shawarwarin dakile gine-ginen ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙarfafa bin dokokin tsara birane.
Gwamnatin ta bai wa kwamitin wa’adin makonni huɗu domin gabatar da rahotonsa.
