Majalisar Ƙaramar Hukumar Bagwai ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar, Injiniya Bello Abdullahi Gadanya, tana sanar da daukacin al’umma musamman matasa cewa, an haramta duk wani nau’in wasan Sallah da ake gudanarwa a bakin Dam ɗin Bagwai.
Wannan mataki ya biyo bayan wani muhimmin zama da aka gudanar tsakanin Shugaban Ƙaramar Hukumar da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da hana duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali ko barazana ga tsaro a lokacin bukukuwan Sallah.
Sanarwar tana ƙara jan hankalin matasa da sauran al’umma da su mutunta wannan doka tare da kaucewa duk wani yunkuri na karya ta, domin duk wanda aka samu ya saɓa da wannan umarni zai fuskanci hukunci mai tsanani daidai da tanadin doka.
Majalisar Ƙaramar Hukumar Bagwai tana kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙaramar hukumar.
Idan kunne ya ji, gangar jiki ya tsira.
Wannan sanarwa ce daga Shugaban Ƙaramar Hukumar Bagwai
Injiniya Bello Abdullahi Gadanya
Ta Hannun Jami’in Yaɗa Labarai
Ƙaramar Hukumar Bagwai. Shehu Bello Shanono.
