Shugaban Amurka Donald Trump ya bar kasar zuwa birnin Beijing na kasar China domin ganawa da shugaban kasar Xi Jinping kan rikicin Iran da ke kara tayar da hankalin duniya.
Kafin tafiyarsa daga Washington, Trump ya shaida wa manema labarai cewa batun kasuwanci ne zai fi daukar hankali a tattaunawar, amma ya ce zai yi “doguwar tattaunawa” da Xi kan halin da ake ciki a Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Iran ke zargin Amurka da Isra’ila da kirkirar hujjoji domin halasta ci gaba da kai hare-hare kan Tehran.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce rikicin da ake yi yanzu tsakanin “al’umma mai mutunci ne da kuma masu yada karya domin tayar da fitina.”
A wani bangare kuma, Koriya ta Kudu ta bayyana cewa tana nazarin yiwuwar mara baya ga kokarin Amurka na tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz bayan da wani jirgin ruwa mai alaka da kasar ya fuskanci hari a makon da ya gabata.
Ministan Tsaron Koriya ta Kudu, Ahn Gyu-back, ya ce kasarsa na duba yiwuwar bayar da jami’ai da kayan aikin soja tare da musayar bayanan sirri domin taimakawa wajen kare mashigin.
Ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Ministan Tsaron Amurka Pete Hegseth a Pentagon.
Rahotanni kuma sun ce wani katafaren jirgin dakon danyen mai na China mai suna Yuan Hua Hu ya ratsa mashigin Hormuz cikin nasara duk da tsananin zaman dar-dar da ake ciki a yankin.
A Lebanon kuwa, rahotanni daga hukumomin kasar sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare a garin Khiam da ke kudancin kasar tare da bude wuta da manyan bindigogi zuwa wasu yankuna da ke kusa.
Haka kuma jami’an agaji a Lebanon sun ce hare-haren Isra’ila sun afkawa motocin daukar marasa lafiya a yankunan Nabatieh da Arnoun, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ma’aikatan ceto.
A Iran kuwa, kafafen yada labaran gwamnati sun tabbatar da kashe wani mutum mai suna Ehsan Afreshteh ta hanyar rataya bayan an same shi da laifin yi wa hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad aiki.
Iran ta ce mutumin ya samu horaswa a Nepal tare da mika bayanan sirrin tsaron kasar ga Isra’ila.
Duk da ci gaba da hare-haren Isra’ila a Gaza, an ga Falasdinawa da yara suna shakatawa a bakin teku a Gaza City yayin tsananin zafi, abin da wasu ke gani a matsayin kokarin ci gaba da rayuwa duk da mawuyacin hali.
