Shugaba Yuweri Kaguta Museveni na kasar Uganda Ya Sake Kafa Tarihi inda a yau Talata a idon duniya ya karkata zuwa birnin Kampala, inda aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Uganda a karo na bakwai.
Wannan rantsuwa ta biyo bayan nasarar da ya samu a zaben watan Janairun 2026, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine.
Museveni, mai shekaru 81, yanzu haka ya kwashe shekaru 40 yana jan ragamar mulkin kasar, lamarin da ya sa ya zama daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan gadon mulki a nahiyar Afirka.
