Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da ta yi amfani da zaɓen gwamnan Jihar Osun wajen nuna yadda ta shirya domin tunkarar babban zaɓen 2027.
Za dai a gudanar da zaɓen ne a yau Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026, inda ’yan takara 15 za su fafata.
Daga cikinsu akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party, ɗan takarar APC, Munirudeen Bola Oyebamiji, da ɗan takarar jam’iyyar ADC, Najeem Salaam.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Tinubu ya buƙaci INEC ta tabbatar da cewa zaɓen ya kasance cikin ’yanci, adalci da gaskiya.
Ya kuma buƙaci masu kaɗa ƙuri’a su fito cikin lumana domin kaɗa ƙuri’unsu, tare da kira ga hukumomin tsaro da su kare masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe.
