’Yan asalin Najeriya masu gudanar da kasuwanci a ƙasar Saudiyya sun buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ƙara samar da matakan da za su sauƙaƙa harkokin kasuwanci tsakanin ’yan Najeriya da takwarorinsu na ƙasashen waje, domin bunƙasa tattalin arziki da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’umma.
Sun ce faɗaɗa kasuwanci zuwa ƙasashen waje na bai wa ’yan kasuwar Najeriya damar shiga sabbin kasuwanni, tare da samar da guraben ayyukan yi musamman ga matasa.
Inda suka ce hakan zai taimaka wajen rage yawan matasan da ke dogaro da gwamnati, tare da ƙara bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar da ke gudanar da harkokinsa tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya, Abdulsamat Sanu Harun Idris wanda yake gudanar da harkar juice, ya ce yanzu haka ya mallaki shaguna 56 a ƙasar Saudiyya, wanda ke nuna cewa akwai babbar dama ga ’yan Najeriya wajen faɗaɗa harkokin kasuwancinsu zuwa ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa samar da ingantaccen yanayi da sauƙaƙa hanyoyin kasuwanci zai taimaka wajen ƙara yawan jarin da ake shigowa da shi ƙasar, tare da samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
