Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su mutunta addinin juna tare da yin aiki tare domin kare Najeriya.
Bala Lau, ya ce bambancin addini bai kamata ya hana ’yan Najeriya zaman lafiya ba, inda ya bayyana cewa Musulmi da Kiristoci duk suna da haƙƙoƙi iri ɗaya a ƙasar nan.
Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a filin jirgin sama na Abuja, bayan kammala wani taron ƙasa da ƙasa na kwanaki biyu kan bambancin ra’ayi da zaman lafiya, wanda JIBWIS ta shirya tare da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya.
Bala Lau ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su koyi darasi daga yadda Annabi Muhammad (SAW), ya zauna lafiya da sauran mabiya addinai a Madina.
Ya ce za a aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron ta hanyar wani kwamiti da zai ƙunshi JIBWIS da Ƙungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya.
Tun da farko, Sakataren-Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya yi gargaɗi kan tsattsauran ra’ayi, tare da kira ga ’yan Najeriya da kada su bari addini, ƙabilanci ko talauci ya raba su.
