Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce tallafawa iyaye mata da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake yi duk wata, tamkar zuba jari ne wajen bunƙasa tattalin arzikin su da rage talauci.
Nantawe ya bayyana haka ne a wajen rabon tallafin ga mata 5,200 da gwamnan ya rabawa naira miliyan 260 domin dogaro da kai.
Farfesa Nantawe wanda ya samu wakilcin Mamban jam’iyyar ta APC a matakin Kasa, Muhammad Jamo Yusuf, ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin mataki dake nuna ƙudirin gwamnatin jihar na inganta rayuwar mata da yaƙi da talauci.
A nasa jawabin gwamna Abba Kabir ya ce ƙarƙashin shirin, mata 5,200 daga ƙananan hukumomi 44 na jihar duk wata, inda Mata 200 daga kowace ƙaramar hukuma 8 na cikin birnin jihar suke amfana, yayin mata 100 daga kowace ƙaramar hukuma 36 na karkara ne ke amfana da tallafin domin kafawa ko faɗaɗa sana’o’insu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamnatin Kano ta bayyana cewa shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren zuba jari da nufin rage talauci, ƙarfafa harkokin tattalin arziki a matakin ƙasa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.
