Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga takarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta wa’adi na biyu.
Shugaban JIBWIS na Kano, Farfesa Abdullahi Saleh, ne ya bayyana hakan lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai masa ziyarar ta’aziyya a gidansa bisa rasuwar matarsa.
Farfesa Abdullahi Saleh ya yabawa gwamnan bisa jagorantar tawagar ta’aziyyar da kansa, yana mai cewa hakan ya nuna tausayi, tawali’u da kuma girmama malamai da shugabannin addini.
Ya ce nasarorin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu a fannoni daban-daban sun dawo da kwarin gwiwar al’umma ga gwamnati, tare da mayar da Kano abin koyi a shugabanci mai anfani ga jama’a.
Shugaban na JIBWIS ya kara da cewa ayyukan ci gaba da gwamnatin ke aiwatarwa na bukatar ci gaba domin kammala manufofin da aka tsara domin cigaban jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, a martanin ds Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar, ya godewa Farfesa Abdullahi Saleh bisa addu’o’i, goyon baya da amincewa da manufofin gwamnatinsa da malamai da shugabannin addini da gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kyawawan dabi’u a tsakanin al’umma.
