A duk ranar 6 ga watan Yuli, ana bikin Ranar Bunƙasa Karkara ta Duniya.
Majalisar ɗinkin Duniya ce ta ware wannan rana domin jaddada muhimmancin raya yankunan karkara a matsayin ginshiƙin samar da abinci, rage talauci da bunƙasa tattalin arziki.
Majalisar ta bayyana cewa fiye da rabin al’ummar Duniya na rayuwa ne a yankunan karkara, inda galibinsu ke dogaro da noma, kiwo da sauran sana’o’in gargajiya domin samun abin masarufi.
Sai dai duk da irin wannan muhimmanci, yankunan karkara na ci gaba da fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ƙarancin hanyoyi, rashin ingantattun cibiyoyin lafiya, matsalolin ilimi, ƙarancin ruwan sha da kuma rashin wadatacciyar wutar lantarki.
Masana na ganin cewa bunƙasa karkara ba wai inganta rayuwar mazauna yankunan kaɗai ba ne, hanya ce ta ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Hakan zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, samar da ayyukan yi ga matasa da rage kwararar al’umma daga karkara zuwa birane.
A Najeriya, noma na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga miliyoyin mutane, musamman mazauna karkara.
Duk da haka, manoma na ci gaba da kokawa kan matsalolin tsadar kayan noma, sauyin yanayi, rashin rance mai sauƙi daga gwamnati da kuma matsalolin tsaro da ke shafar ayyukansu.
