Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da tsarin tattara bayanan gudanar da harkokin Kiwon dabbobi a jihar, domin zamanantar da harkokin kiwo da sauƙaƙa ayyukan da suka shafi masu kiwon dabbobi.
Kwamshinan Ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi ta Kano Dr Aliyu Isa Aliyu ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da shirin bisa jagorancin Ministan raya kiwon dabbobi na Najeriya Alhaji Idi Mukhtar Maiha, a asibitin dabbobi na Gwale.
Dr Aliyu ya ce ƙaddamar da tsarin wani babban ci gaba ne a ƙoƙarin gwamnatin Kano na mayar da harkokin kiwo zuwa tsarin zamani na fasahar sadarwa.
A cewarsa, ta hanyar wannan tsarin, masu kiwon dabbobi za su iya yin rajistar gonakinsu, neman ayyuka da tallafin likitocin dabbobi, bayar da rahoton bullar cututtuka, neman allurar rigakafi, samun lasisi, da kuma cin gajiyar sauran ayyukan da aka tanada ta hanyar intanet a https://mld.kn.gov.ng/.
Kwamishinan ya ƙara da cewa tsarin zai tattara bayanai kai tsaye daga kasuwannin dabbobi, wuraren kiwo, wajen yanka dabbobi, asibitocin dabbobin da kuma shirye-shiryen rigakafin dabbobi a faɗin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishinan na godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa goyon baya da amincewar da yake baiwa ma’aikatar, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tukuru domin gina fannin kiwo na zamani, a karkashin manufofin “Kano First”.
