Shugaban Kwalejin Nazarin shari’a da addinin Musulunci ta Kano wato LEGAL, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ya mika ragamar jagorancin kwalejin ga Mataimakinsa mai kula da harkokin ilimi Dr Ali Tamasi Mu’az, bayan kammala wa’adinsa na biyu a ofis.
Da take jawabi yayin taron mika ragamar, magatakardar kwalejin, Raliya Aliyu Abubakar, ta bayyana Farfesa Jakada a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda gudummawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihin kwalejin.
Da yake jawabi, yayin mika ragamar Farfesa Jakada ya godewa mahukunta da ma’aikata da dalibai bisa hadin kai da goyon bayan da suka bashi, yana mai cewa rahoton mika mulkin ya kunshi bayanai da shawarwari domin ci gaban kwalejin.
Shima sabon shugaban rikon Dr Ali Tamasi Mu’az, ya yabawa tsohon shugaban bisa jagoranci da gudummawar da ya bayar, tare da tabbatar da kudirinsa na ci gaba da dorewar nasarorin da ake samu a kwalejin.
