Mataimakin Shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci al’ummar arewacin Najeriya, da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, domin rama goyon bayan siyasa da ya bai wa ’yan takarar shugaban ƙasa daga yankin na arewa a baya.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu a Kaduna, inda ya buƙaci al’ummar Arewa su ci gaba da marawa jam’iyyar APC baya, la’akari da yadda ta himmatu wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa da kawo ci gaba, musamman a yankin na Arewa.
Kashim ya ce goyon bayan Tinubu ya samo asali ne daga amana, biyayya da kuma rama alheri, yana mai tunatar da al’ummar arewa cewa Tinubu ya goyi bayan Atiku Abubakar a 2007, Nuhu Ribadu a 2011, sannan Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da 2019, wanda hakan ya ba shi damar samun wa’adi na biyu.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kamata arewa ta tuna da waɗanda suka tsaya mata a lokacin da shugabanninta ke neman shugabancin ƙasa, yana mai bayyana goyon bayan da ake bai wa Tinubu a matsayin wani lamari da ya shafi mutunci da cika alƙawari.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shettima na bayyana wasu ayyukan gwamnatin tarayya a arewa, da suka haɗa da bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano, ayyukan layin dogo da manyan hanyoyi, ciki har da hanyar Abuja zuwa Kaduna, Zariya da Kano, tare da zuba jari a fannin ilimi da koyar da sana’o’i, da nufin samar da ayyukan yi, faɗaɗa damar tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
