Tsohon Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ya san makamar aiki kuma ya nuna wa ’yan Arewa cewa yana tare da su.
Sheikh Pakistan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa, inda ya jaddada cewa yana da ’yancin goyon bayan duk ɗan takarar da yake ganin ya dace a matsayinsa na ɗan Najeriya.
Malamin ya ce ya kamata ’yan Arewa su yi wa Shugaba Tinubu adalci, bisa la’akari da irin goyon bayan da ya ce shugaban ya nuna musu a baya.
Kalaman Sheikh Pakistan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan goyon bayan da wasu malaman addini ke bai wa ’yan siyasa a Najeriya, musamman dangane da rawar da ya kamata malamai su taka a harkokin mulki da zaɓen shugabanni.
