Dan takarar shugaban kasa a jam’yyar ADC Atiku Abubakar ya mayar wa da Tinubu martani kan kalaman sa ne cewa ƴan adawa ne su ka ƙirƙiri yunwa a Nijeriya
Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin kauce wa alhakin matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta, bayan shugaban ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya kwatanta maganar Tinubu da mutumin da ya kunna wuta sannan ya zargi maƙwabtansa da hayaƙin da ta haifar.
Atiku ya ce jam’iyyar APC ta shafe shekaru takwas tana mulkin Najeriya kafin Tinubu ya hau karagar mulki, kuma gwamnatin yanzu ta ƙara kusan shekaru uku da rabi, don haka bai kamata ta ɗora wa ’yan adawa alhakin matsin rayuwa ba.
Ya tambayi gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur, faduwar darajar naira, ƙaruwar talauci da matsalar tsaro da suka haɗa da kashe-kashe, garkuwa da mutane da korar al’umma daga muhallansu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayoyi kan wasu kuɗaɗen gwamnati da ya ce suna buƙatar bayani, ciki har da kashe-kashen da suka shafi tsaron makamashi da ayyukan bututun mai na NNPC.
Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati bisa yanayin rayuwar ’yan Najeriya, ba wai bayanan da take bayarwa a wajen tarukan siyasa ba.
Ya bayyana zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin damar da ’yan Najeriya za su yi amfani da ita wajen yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin Tinubu.
