Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya rika magana kai tsaye da ‘yan kasar nan kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa, maimakon ya dogara da mataimakansa da masu magana da yawunsa.
Ndume ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Tinubu.
Ya ce ya dace ‘yan Nijeriya su ji daga bakin shugabansu kai tsaye, musamman kan matsalolin tattalin arziki da kuma matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara.
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce matsalar tsaro na buƙatar matakan gaggawa da haɗin gwiwa.
Ya kuma bayyana fatan cewa sabbin hare-haren da sojoji ke kai wa ‘yan bindiga za su haifar da ɗorewar zaman lafiya.
A cewarsa, a halin yanzu jami’an tsaro sun ƙara matsa lamba kan ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke aiki a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan.
Ndume ya yabawa Shugaba Tinubu kan yadda yake tunkarar matsalar tsaro, yana mai cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna gwamnatin ta ƙara himma wajen magance ƙalubalen.
