Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar an hukunta duk waɗanda aka kama da hannu a sace ɗalibai da malamansu a jihar Oyo, tare da waɗanda ke da hannu a kisan Mista Oyedokun.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake taya jami’an tsaro murnar nasarar da suka samu wajen ceto ɗaliban da malamansu da aka sace bayan shafe kwanaki 56 suna hannun masu garkuwa da mutane.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yabawa sojoji, jami’an DSS da ‘yan sanda bisa gudanar da aikin ceto ba tare da rasa ran ko ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ba.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kashe aƙalla ‘yan bindiga tara tare da kama mutum takwas a wani samame na haɗin gwiwa da suka kai bisa bayanan sirri da DSS ta tattara.
An sace aƙalla ɗalibai da malamai 45 ne bayan harin da ‘yan bindiga suka kai makarantu uku a yankin Ogbomoso da ke ƙaramar hukumar Oriire a ranar 15 ga watan Mayu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumomin agajin gaggawa da gwamnatin jihar Oyo da su samar wa waɗanda aka ceto kulawar lafiya da sauran tallafin gaggawa da suke buƙata.
