Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar da fara aiwatar da sabon matakin toshe zirga-zirgar jiragen ruwa da ke hulɗa da Iran, daga yau Talata.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, CENTCOM ta bayyana cewa matakin zai shafi dukkan jiragen ruwa da ke shiga ko fita daga tashoshin jiragen ruwa da yankunan gabar tekun Iran.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ba sauran jiragen ruwa kariya domin tabbatar da zirga-zirgarsu cikin aminci, matuƙar ba su karya dokokin takunkumin da Amurka ta gindaya ba.
Tun da farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta sake ƙaƙaba takunkumi kan jiragen ruwa masu hulɗa da Iran, a wani yunƙuri na ƙara matsin lamba kan Tehran.
CENTCOM ta ce sabon matakin ya yi kama da wanda Amurka ta aiwatar tsakanin 13 ga Afrilu zuwa 18 ga Yuni, wanda ya takaita zirga-zirgar jiragen ruwa masu alaƙa da Iran.
Wannan sanarwa ta zo ne jim kaɗan bayan Iran ta bayyana rufe Mashigar Hormuz na ɗan lokaci, sakamakon sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin Tehran da Washington, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya kan makomar zirga-zirgar man fetur da kasuwanci a yankin.
