
Babbar kotun jiha mai lamba 13 da ke Miller road, karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusif, ta sanya ranar 15 ga watan Mayun 2025, domin sauraron karar da wani mutum mai Suna Faisal Abdulmunaf ya shigar da gwamnatin Kano kan batun rushe masa gidaje guda goma da ta yi.
Ya ce biyar daga cikin gidajen sun kai matakin hawa na biyu, biyar kuma suna matakin farko wato foundation, wadanda ke kan titin Mukhtar Muhammed link daura da babban titin Ahmadu Bello Way.
Mai karar ta bakin lauyansa, ya bayyana wa kotun cewa wadanda ake kara sun rushe masa gidajen duk da cewar ya cika duk wata ka’ida ta mallakar filayen tare da cika dokokin ma’aikatar hukumar kula da filaye da tsara birane.
Mai korafin ya gabatar da wasu takardun mallaka da satifiket mai lamba LKN/COM/2002/485/LKN/2002/487 da ke kunshe da shaidar filayen daga na daya zuwa na goma.
A takardun karar shafi na biyu sadara ta 4 da ta 5 da ta 6, mai karar ya roki kotun ta sanya gwamnatin jihar Kano ta biya shi Naira biliyan uku da miliyan dari shida da tamanin da bakwai da dubu dari takwas da tara da dari takwas da ashirin da takwas da kobo sittin da bakwai a matsayin diyya.
Sai kuma Naira biliyan daya da ya roki a biya shi sakamon tashin hankalin da ya ce ya hadu da shi.
Mai karar ya kuma nemi a biya shi Naira miliyan dari biyu kudin a matsayin kudin haya mafi kankanta da ya kamata ya samu duk shekara akan wadannan gidajen guda goma.
Ya kuma roki kotun, ta hana gwamnatin jiha ko wasu wakilanta daga yin amfani da wajen da ake magana akansa.
Kotun dai ta sanya ranar 15 ga watan Mayun 2025 domin sauraron kowanne bangare domin ci gaba da shari’a da kuma bayyana matsayarta kan shari’ar.