Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar tsaro mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU) domin magance manyan laifuka a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an kafa cibiyar ne domin yaƙi da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka, yayin ƙaddamar da ita a Metro Division da ke Kano.
A cewarsa, an zaɓi ƙwararrun jami’an ’yan sanda da aka bawa horo na musamman domin gudanar da ayyukan cibiyar, wadda ya ce wani sabon tsari ne na babban sufeton ’yan sanda na daƙile muggan laifuka.
