Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Najeriya ta tura dakarun sojoji zuwa Benin domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka a yankin Afirka ta Yamma.
Ya bayyana hakan ne a wani taron shekara-shekara na hafsoshin rundunar sojin ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce rundunar na ci gaba da haɗa kai da ƙasashen maƙwabta wajen musayar bayanan sirri da ayyukan tsaro.
Shu’aibu ya ce matakin na nuna ƙudirin Najeriya na ƙarfafa tsaron yankin, tare da yabawa Bola Ahmed Tinubu kan goyon bayan da yake bai wa rundunar soji ta fuskar kayan aiki da walwalar jami’ai.
Ya kuma ce an inganta kayan yaƙi, matsugunan sojoji da alawus domin ƙarawa dakarun ƙwarin guiwa.
