Rundunar Sojin kasarnan ta ladabtar da wani soja da ke aiki a ƙarƙashin Operation Hadin Kai bayan ya wallafa wani rubutu da hoto a kafafen sada zumunta game da yanayin abincin da ake bai wa dakarun da ke yankin Arewa maso Gabas.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in yada Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanal Sanni Uba, ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce matakin ya biyo bayan bincike na cikin gida da aka gudanar sakamakon hoton da ya bazu a shafukan sada zumunta.
Uba ya bayyana cewa rundunar ta duba abin da aka wallafa tare da hoton da sojan ya yada, inda ta gano cewa bai bayyana cikakken yanayin yawan abincin da aka ba shi ba a lokacin da ya dauki hoton hakan yasa alumma suka fara zargin ba’a wadata dakarun rundunar da abincin da ya dace.
Ya ce bayan cikakken bincike, hedikwatar tsaro ta ƙaryata ikirarin da ke yawo, tana mai cewa ba su wakilci gaskiyar tsarin abinci da walwalar dakarun da ke yankin ba.
A cewarsa, dakarun Operation Hadin Kai na samun abinci bisa ƙa’idojin da aka amince da su, tare da ci gaba da inganta walwalar su musamman a lokutan bukukuwa irin su Sallah da Easter domin ƙara musu ƙwarin gwiwa.
Uba ya ƙara an ɗauki matakan ladabtarwa bisa tanadin Dokar Sojoji domin tabbatar da ladabi da kare martabar rundunar.
Ya shawarci dakarun da su riƙa amfani da hanyoyin cikin gida da aka tanada wajen kai ƙorafe-ƙorafe, maimakon amfani da kafafen sada zumunta da ka iya ɓata gaskiyar al’amura ko rage ƙwarin gwiwar sojoji.
