
Aminu Abdullahi Ibrahim
Rikicin ƙungiyar tuntuba ta Arewa, Arewa Consultative Forum (ACF), na ƙara tsananta, Kwamitin Zartarwar kungiyar (NEC) ya bayyana karin dalilan da suka sa ya dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da kuma keta kundin tsarin mulkin ƙungiyar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya sanya wa hannu bayan taron da aka gudanar a Kaduna, an ce kwamitin ya kuma kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da shugabancin sa tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken binciken kan kuɗaɗen ƙungiyar.
Sanarwar ta ce duk da cewa jami’an ‘yan sanda dauke da makamai sun rufe sakatariyar ƙungiyar da ke Kaduna, shugabannin ACF sun koma wani wuri inda suka gudanar da taron cikin sirri.
Kwamitin ya ce matakin binciken kuɗaɗen ACF ya biyo bayan amincewa da shawarwarin Kwamitin Ladabtarwa da Da’a wanda ya binciki zarge-zargen da ke cikin wata takarda korafi da aka shigar kan Alhaji Bashir Dalhatu.
