Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Monday, April 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRashin tarbiyya ne sanadin matsalolin Arewa –Arewa Youth

Rashin tarbiyya ne sanadin matsalolin Arewa –Arewa Youth

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Adaidai lokacin da ake fuskantar kalubale a fannoni daban-daban na kasar nan, kungiyoyin matasa na cigaba da fadakar da matasa don ganin goben alummar kasar nan tayi kyau.

 

Kungiyar Arewa Youth Good Character na cikin kungiyoyin dake aiki tukuru don ganin tarbiyyar matasa a yankin Arewa tayi kyau, domin cigaban yankin.

 

Shugaban kungiyar na kyautata tarbiyya da cigaban matasan Arewan Nura Ali Abdullahi Mai-Dile yace dukda arzikin da Allah yayiwa Arewacin Najeriya rashin tarbiyya ya zama wani kalubale da ya haddasa kusan dukkanin matsalolin da yankin ke fuskanta.

 

Dayake tsokaci kan matsalar tsaro yayin wata ziyara da ya kawo Premier Radio Ali Abdullahi yace suna aikin wayar da kan matasa da su rungumi zaman lafiya domin hakan ne zai taimaka wurin cigaban wannan yanki.

 

Yankin Arewa dai na fuskantar tarin kalubale musamman matsalar tsaro da taki ci taki cinyewa, abinda yasa masu ruwa da tsaki a yankin suketa kiraye-kiraye ga alummar kan hanyoyin da za’abi don lalubo bakin matsayi

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories