Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiINEC: fiye da mutane miliyan bakwai ba a dauki hotonsu da na...

INEC: fiye da mutane miliyan bakwai ba a dauki hotonsu da na ‘yan yatsu ba

Date:

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace fiye da ‘yan kasar nan miliyan bakwai ne suka yi rijistar katin zabe ta Internet amma basu je cibiyoyin hukumar don daukar hotunan su dana ‘yan yatsun suba.

 

Tun a watan Yunin shekarar 2021, ne hukumar zaben ta fara yin rijistar sabon katin zabe tare da kaddamar da shafin Internet da wanda mutane zasu iya cike bayanan su tare da zuwa daya daga cikin ofisoshin hukumar domin kammala yin rijistar.

 

Bayan mutum ya cike bayanan sa dai ya kanje ofishin hukumar ta INEC don a dauki hoton sa dana ‘yan yatsu.

Bayan barazanar tsigeshi Buhari ya kira taron tsaro na gaggawa.

Haka zalika hukumar ta gargadi jam’iyyun siyasa a kasar nan dasu kaucewa karya dokokin hukumar na fara yakin neman zabe tun kafin wa’adin faraway ya cika.

Rashin tsaro ya janyo karancin masu karbar katin zabe a Katsina-INEC

Cikin jadawalin da hukumar INEC ta fitar a farkon wannan shekarar ya nuna cewa za a fara yakin neman zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar tarayya a ranar 28 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki.

 

Yayin da ‘yan takarar gwamna dana majalissun jihohi zasu fara nasu yakin neman zaben a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar da muke ciki.

 

Haka zalika za’ayi zaben shugaban kasa dana ‘yan majalissun tarayyar kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, inda zaben gwamna dana majalissun jihohi za a yi shi a ranar 11 ga watan Marish na shekarar ta 2023.

Latest stories

Related stories