24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiFRSC za ta fara kama babura marasa lamba

FRSC za ta fara kama babura marasa lamba

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa FRSC ta bada umarnin kama babura marasa lamba dake kai da komo a sassan kasar nan.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa matakin ya biyo bayan wani rahoto da aka wallafa kan yadda ababen hawa marasa lamba ke zarya a titunan Abuja, duk da haramcin hakan a bisa doka.

Mukaddashin shugaban hukumar, Dauda Ali Biu tuni ya umarci kwamandojin su 37 da su fara aikin tabbatar da dokar nan take.

Ya alakanta hakan  da kokarin kyautata sha’anin tsaro.

A wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, tace umarnin zai taimaka wajen tilastawa masu ababen hawa yin rajista, domin shigar da bayanan su cikin kundin kasa.

Tuni dai rahotanni ke bayyana yadda yan tada kayar baya ke amfani da babura masu kafa 2 wajen kai hare-hare, abinda yasa a baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta yunkuro da nufin haramta hawa baburan a fadin kasar nan.

Latest stories