Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta idan suka lashe zaɓen 2027.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da magoya baya da masu ruwa da tsaki a birnin Enugu, inda ya ce gwamnatinsu za ta ba da muhimmanci na musamman ga tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma yi alƙawarin ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi, domin magance matsalar miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da inganta tsarin ilimi a faɗin ƙasar.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.
Ya kuma yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su yi taka-tsantsan da farfagandar siyasa, tare da tantance manufofin ’yan takara kafin yanke shawara a zaɓen 2027.
A nasa ɓangaren, abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da bambance-bambancen ƙabilanci, su haɗa kai domin kawo sauyi a ƙasar.
Kwankwaso ya ce Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro, talauci, yunwa da rashin aikin yi, waɗanda a cewarsa suke buƙatar shugabanci mai inganci domin magance su.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su fito domin kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen 2027, tare da bin hanyoyin da doka ta tanada wajen sa ido kan ƙuri’unsu har zuwa lokacin bayyana sakamakon zaɓe.
