Gwamnatin Jihar Kano ta rantsar da sabbin manyan sakatarori 19, kwamishinoni shida da masu ba gwamna shawara uku, a wani mataki na ƙarfafa gudanar da ayyukan gwamnati a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bikin rantsarwar da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation da ke Fadar Gwamnatin Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan ya bayyana cewa an rantsar da sabbin kwamishinonin ne bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance su tare da amincewa da naɗinsu.
Sabbin kwamishinonin sun haɗa da Salisu Yusha’u, soja mai ritaya, wanda zai jagoranci Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida, da Idris Garba Unguwar Rimi, wanda aka bai wa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
Sauran sun haɗa da Mukhtar Ishaq Yakasai, wanda zai jagoranci Ma’aikatar Jin Ƙai, da Ibrahim Ali Namadi Dala, wanda zai kula da Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari.
Haka kuma, an naɗa Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa a matsayin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, yayin da Farfesa Sani Lawan Malumfashi zai jagoranci Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi.
A wani ɓangaren kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatunsu, inda tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya koma Ma’aikatar Matasa da Wasanni.
Shi kuwa tsohon Kwamishinan Ma’adanai, Safiyanu Kachako, an mayar da shi Ma’aikatar Muhalli.
Wakilin Premier Radio, Kamal Umar Kurna, ya ruwaito cewa mata tara ne daga cikin manyan sakatarori 19 da aka rantsar.
Sabbin jami’an sun yi alƙawarin gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, domin sauke nauyin da aka ɗora musu.
