Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yunƙurin ci gaba da karɓo basussuka daga ƙasashen waje, yana mai nuna damuwa kan yadda Najeriya ke tafiyar da manufofinta na tattalin arziki.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin wani taron tattaunawa da jama’a da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce bai kamata Najeriya ta riƙa aiwatar da shawarwarin masana tattalin arziki da suka yi karatu a ƙasashen waje kai tsaye ba, ba tare da tantance dacewarsu da yanayin tattalin arziki da buƙatun al’ummar ƙasar ba.
A cewarsa, akwai buƙatar Najeriya ta samar da hanyoyin magance matsalolinta bisa la’akari da halin da take ciki, maimakon dogaro kacokan da tsare-tsaren da aka tsara domin wasu ƙasashe.
Obasanjo ya kuma bayyana muhimmancin amfani da fasahar basirar wucin gadi (AI) wajen magance matsalolin al’umma, musamman a matakin ƙananan hukumomi.
Ya ce tattaunawar za ta taimaka wajen gano hanyoyin amfani da fasahar domin inganta ayyukan gwamnati da samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
