Gwamnatin Kano ta rantsar da sabbin manyan sakatarori 19, da masu baiwa gwamna shawara guda 3 da kuma kwamishinoni 6, domin ƙarfafa gudanar da ayyukan gwamnati da tabbatar da ingantaccen aikin ma’aikatun gwamnati a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci rantsar da sabbin jami’an, yayin wani taro da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin ta Kano, inda Gwamnan ya ce rantsar da kwamishinonin 6, ya biyo bayan tabbatar da naɗinsu da majalisar dokokin jihar ta yi.
Sabbin kwamishinonin sun hada da Salisu Yusha’u soja mai ritaya, wanda zai jagoranci ma’aikatar tsaron cikin gida, yayin da Idris Garba Unguwar Rimi zai jagoranci ma’aikatar ayyuka na musamman, sai Mukhtar Ishaq Yakasai wanda zai jagoranci ma’aikatar jin ƙai, yayin da Ibrahim Ali Namadi Dala ya samu ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa kuwa zai jagoranci ma’aikatar kimiyya da fasaha, yayin da Farfesa Sani Lawan Malumfashi zai jagoranci ma’aikatar ilimi mai zurfi.
Gwamna Abba ya kuma sauyawa wasu kwamishinoni daga ma’aikatun su inda tsohon kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Waiya ya koma ma’a’aikatar matasa da wasanni yayin tsohon kwamishinan ma’aikatar ma’adanai Safiyanu Takai ya koma ma’aikatar Muhalli.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa sakatarorin da gwamnan ya rantsar guda 9 mata ne, lamarin da ya nuna yadda mata ke samun gurbi a manyan muƙaman gudanarwa na gwamnatin jihar, inda dukkan su suka yi alƙawarin yin aiki da gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
