Majalisar Dokokin Najeriya na nazarin wani ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai samar da ƙarin kujeru 74 na musamman ga mata a Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana hakan ranar Litinin yayin taron makon shari’a na ƙungiyar lauyoyi mata ta ƙasa (FIDA) a Jihar Ekiti.
Bamidele ya ce ƙudirin ya tanadi ƙarin kujeru 37 a Majalisar Dattawa da 37 a Majalisar Wakilai, inda kowace jiha da Babban Birnin Tarayya Abuja za su samu kujera ɗaya a kowace majalisa.
Ya ƙara da cewa ana kuma shirin samar da ƙarin kujeru uku na mata a kowace Majalisar Dokokin Jiha.
A cewarsa, tsarin zai ɗauki shekaru 16, kwatankwacin wa’adin zaɓe huɗu, kafin a sake nazarinsa.
Sanatan ya bayyana cewa manufar ƙudirin ita ce ƙara yawan mata a harkokin siyasa da shugabanci, ba tare da rage kujerun da ake da su a halin yanzu ba.
Sai dai ya ce sai an samu amincewar da kundin tsarin mulki ya tanada daga Majalisar Ƙasa da majalisun dokokin jihohi kafin ƙudirin ya zama doka.
