Jam’iyyar APC a Kano ta yi watsi da zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na cewa APCn da ɗan takarar ta na gwamna, Abba Kabir Yusuf, suna da hannu wajen yunƙurin cire ɗan takarar gwamna na NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin ‘yan takarar zaɓen 2027.
Shugaban jam’iyyar APCn a Kano Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda sanarwar ta bayyana zargin a matsayin marar tushe balle makama.
Jam’iyyar ta ce shari’ar ta samo asali ne daga rikicin cikin gida na NDC, inda wasu mambobin jam’iyyar suka shigar da ƙara a kanta, ba APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf ko gwamnatin Kano ba.
APCn ta ce yunƙurin danganta ta da shari’ar na nufin karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da ke cikin NDC, tare da ƙalubalantar Kwankwaso da ya gabatar da sahihan hujjoji da za su tabbatar da zargin, maimakon yin kalaman da za su iya yaudarar jama’a da haifar da rikicin siyasa.
Jam’iyyar APCn ta kuma jaddada cewa kotuna a Najeriya masu zaman kansu suke yi, kuma babu jam’iyya ko ɗan takarar da ke da ikon rinjayar hukuncinsu, tana mai cewa duk ɗan takarar da ya cancanta yana da ‘yancin shiga zaɓe bisa doka.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito sanarwar na cewa Jam’iyyar ta sake tabbatar da goyon bayanta ga tsarin dimokuraɗiyya da shiga zaɓe na jam’iyyun hamayya, tare da kira ga Kwankwaso da sauran ‘yan siyasa da su bar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da ayyukansu ba tare da siyasantar da shari’ar da ta samo asali daga rikicin cikin gida ba.
