Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, ta bayyana cewa za ta jira hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kafin ɗaukar mataki kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC.
Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ya ce hukumar ta samu sanarwar cewa ɓangaren tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke shugabancinsa.
Ya bayyana cewa hukumar za ta yi la’akari da ƙarar da ke gaban kotu kafin yanke matsaya kan shugabancin jam’iyyar.
Sai dai ɓangaren ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya buƙaci INEC ta aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya na ranar 5 ga Nuwamba, 2026.
Ɓangaren ya ce ya kamata hukumar ta cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola daga bayanan hukumar a matsayin shugabannin jam’iyyar, tare da soke sunayen ’yan takarar da ɓangaren Mark ya gabatar.
Shugaban kwamitin amintattu na ɓangaren Gombe, Rufus Ikanmi, ya ce hukuncin kotun yana nan daram, yana mai cewa ba a dakatar da aiwatar da shi ko soke shi ba.
Rikicin ya samo asali ne daga hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu, wanda ya soke shugabancin riƙon ƙwarya na David Mark.
Sai dai ɓangaren Mark ya ɗaukaka ƙara tare da neman kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin.
