An bayyana sharuɗɗa da hanyoyin neman tallafin naira dubu 100 da wani shiri mai suna Nigeria Family Strengthening and Development Programme, NFSP, ke tallatawa ga iyalan da ke fama da matsin tattalin arziki a Najeriya.
A cewar wata sanarwa da hukumar gudanar da shirin ta bayar, tallafin na da nufin rage wa iyalai raɗaɗin tsadar rayuwa, musamman sakamakon hauhawar farashin abinci da sauye-sauyen tattalin arziki.
Sharuɗɗan da aka bayyana sun haɗa da kasancewa ɗan Najeriya ta haihuwa, mallakar lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN, da kuma kasancewa tsakanin shekaru 18 zuwa 65.
Rahoton jaridar PUNCH ya ce an bayyana shafin nfsp.ng/signup a matsayin hanyar rajista, inda masu neman tallafin za su gabatar da bayanansu domin tantancewa.
Masu gudanar da shirin sun ce za a zaɓi waɗanda suka cancanta ne bisa halin talauci da buƙatarsu, ta hanyar tantance bayanan iyalai da lambobin shaidar ɗan ƙasa. Za a gudanar da zaɓen a matakai a shiyyoyin siyasar Najeriya shida.
A cewar masu shirin, waɗanda aka zaɓa za su karɓi saƙon SMS kafin a tura kuɗin zuwa asusun bankinsu. Sun kuma yi gargaɗin kada jama’a su biya kowa kuɗi domin a saka sunansu cikin jerin masu cin gajiyar tallafin.
Sai dai har yanzu akwai buƙatar tabbatar da sahihancin shafin rajistar kai tsaye daga hukumomin gwamnatin tarayya. Saboda haka, ana shawartar jama’a kada su gabatar da bayanan sirri ko na banki kafin samun wannan tabbacin.
